Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kofi Annan Ya Ce Har Yanzu Ana Iya Kaucewa Yaki - 2003-02-24


Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, MDD, Kofi Annan, ya shaidawa taron kolin kasashe masu tasowa cewa har yanzu ana iya kaucewa farmakin soja kan Iraqi a karkashin jagorancin Amurka.

A cikin jawabin da yayi gaban taron kolin kungiyar Kasashen 'Yan Babu-Ruwanmu mai wakilai 116 a Malaysia, Mr. Annan yayi kashedin cewa duk wani farmakin sojan da za a kai a kan Iraqi zai zamo haramun idan ba MDD ce ta bada izninsa ba.

Kafin a kammala wannan taron kolin kwanaki biyu gobe talata a birnin Kuala Lumpur, ana sa ran shugabannin kasashe 50 da wakilan sauran kasashen zasu amince da wani kuduri wanda zai bayyana adawa da kai farmakin soja kan Iraqi ba tare da iznin MDD ba, tare da yin kira ga Iraqi da ta mutunta kudurorin MDD na lalata muggan makamanta.

A lokacin da aka bude taron kolin yau litinin, sabon shugaban kungiyar kasashen babu-ruwanmu, Firayim Minista Mahathir Mohammed na Malaysia, ya soki Amurka a saboda barazanar far ma Iraqi da yaki. Har ila yau Malam Mahathir ya zargi kasashen yammaci da laifin fakewa da yaki da ta'addanci domin mamaye duniya.

Firayim ministan na Malaysia ya ce ya kamata a haramta yaki, yana mai cewa ya kamata MDD ta tabbatar da yin aiki da wannan haramci ta hanyar girka sojoji na kasa da kasa.

XS
SM
MD
LG