Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Amurka Da Britaniya Sun Kara Kutsawa Can Cikin Iraqi - 2003-03-21


Jami'an ma'aikatar tsaron Amurka sun ce sojojin Amurka sun kwace wasu muhimman filayen jirgin sama a yammacin Iraqi, yayin da sojojin Amurka da na Britaniya suka kara nausawa cikin kudancin Iraqi.

jami'an Amurka sun ce an kwace wadannan filayen jirgin sama a yau Jumma'a ba tare da gwabza wani mummunan fada ba.

A can wani gefen kuwa, sojojin kawance sun nausa ta cikin hamada, suka dirkaki Bagadaza, babban birnin kasar, yayin da wasu sojojin suke gwabza fadan kama birnin Umm Qasr dake bakin teku, da kuma Basra, birni na biyu wajen girma a Iraqi. Sojojin Britaniya sun kama mashigin ruwan Faw dake bakin tekun Parisa.

Jami'an sojan Amurka sun bada rahoton mutuwar farko ta wani sojan kundumbalar Amurka wanda aka kashe a lokacin da ake dauki-ba-dadi a kudancin Iraqi.

Wasu Amurkawa hudu tare da sojojin Britaniya takwas sun mutu yau Jumma'a a lokacin da jirgin yakinsu na helkwafta ya fadi a arewacin Kuwaiti.

Firayim minista Tony Blair na Britaniya ya ce wannan yaki yana tafiya yadda suke so, amma kuma ya ce ba zasu iya samun nasara cikin dare guda ba.

XS
SM
MD
LG