Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Akalla 150 Sun Mutu A Nutsewar Jirgin Ruwa A Tabkin Tanganyika - 2003-03-24


Ana fargabar cewa mutane akalla 150 sun mutu a lokacin da wani jirgin ruwan jigilar fasinja ya birkice ya nutse a tabkin Tanganyika a yankin tsakiyar Afirka.

Jami'ai sun ce wannan jirgi ya nutse ranar asabar da maraice a tsakanin wasu garuruwa biyu masu tashar jiragen ruwa a yankin gabashin Kwango-ta-Kinshasa.

Jirgin ruwan ya taso daga garin Kalemie dake hannun 'yan tawaye, ya doshi arewa zuwa lardin Uvira a kasar. Jirgin ya birkice dab da garin Nyanza-Lac dake bakin tabkin, a yankin ruwan kasar Burundi.

An ce mayakan ruwan kasar Burundi sun ceto mutane 41. An bada rahoton cewa jirgin ruwan yana dauke da mutanen da suka zarce kasa da 100 da aka kayyade masa dauka.

Wannan tabki na Tanganyika yana iyaka da kasashen Kwango-ta-Kinshasa da Burundi da Tanzaniya da kuma Zambiya.

XS
SM
MD
LG