Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Taron Dangi Sun Doshi Bagadaza - 2003-03-25


Sojojin taron dangi karkashin jagorancin Amurka sun nausa zuwa kilomita 80 daga birnin Bagadaza, yayin da jiragen saman kai farmaki na taron dangi suka kai hare-hare kan sansanonin zaratan sojojin Iraqi da ake kira Republican Guards a birnin.

Wakilin Muryar Amurka dake hedkwatar sojojin taron dangi a daular Qatar ya ce duk da wannan nausawa da suka yi, sojojin na Amurka suna fuskantar turjiya a kudancin Iraqi.

Jami'an taron dangi suka ce sojojinsu sun kama garin Umm Qasr mai tasoshin jiragen ruwa dake da matukar muhimmanci ga ayyukan jigilar kayayyaki na agaji da za a yi cikin makonnin dake tafe.

'Yan jarida dake tafiya tare da sojojin Amurka sun fada a yau talata cewa sojojin taron dangi suna rike da wasu cibiyoyi masu muhimmanci a Nasiriyya, ciki har da wasu gadoji biyu da suka tsallaka kogin Euphrates. A wannan gari ne sojojin taron dangi suka gamu da turjiya mafi tsanani tun barkewar yakin na Iraqi.

Kakakin sojojin Britaniya, Guruf Kyaftin Al Lockwood, ya ce wannan turjiya ba ta hana sojojin taron dangi dirkakar birnin bagadaza ba. Ya ce "abinda masu kallon telebijin suke gani, kananan artabu ne. Dabararmu ta yaki tana tafiya kamar yadda muka tsara. Zamu fuskanci irin wannan artabu a duk lokacin da suka kunno kai, amma ba zasu hana mu kaiwa ga inda muka dosa ba."

XS
SM
MD
LG