Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Hare-Haren Bam Masu Tsanani Kan Gine-Ginen Gwamnati A Bagadaza - 2003-03-28


Sojojin taron dangi sun yi ta ruwan bama-bamai kamar da bakin kwarya kan gine-ginen gwamnati a Bagadaza, inda aka ga hayaki baki kirin yana tashi a samaniyar babban birnin na Iraqi.

Jami'an sojan Amurka suka ce makamai masu linzami samfurin Tomahawk sun ragargaza cibiyoyin sarrafa ayyukan sojan Iraqi. Sauran cibiyoyin da aka ragargaza sun hada har da na sadarwa da sansanonin zaratan sojojin kasar da ake kira Republican Guard.

'Yan jarida a birnin Bagadaza sun ce hare-haren daren jiya sune mafi tsanani a kan birnin, tun ranar Jumma'ar da ta shige, lokacin da sojojin taron dangi suka kaddamar da kai hare-hare ta sama ka'in da na'in.

Jami'an sojan Amurka suka ce wani jirgin yaki kirar B-2 ya sako dirka-dikar bama-bamai, kowanne mai nauyin fiye da kilo dubu biyu, na ragargaza dakunan karkashin kasa, domin lalata wata cibiyar sadarwa.

Ministan yada labaran Iraqi, Mohammed Saeed al-Sahaf, ya ce hare-haren bam da sojojin taron dangi suka kai kan Bagadaza da Najaf ya kashe fararen hula 33, ya raunata wasu da dama a cikin dare.

Wani kakakin rundunar sojojin Amurka a Qatar ya shaidawa 'yan jarida a yau Jumma'a cewa jiragen taron dangi sun lalata hedkwatocin jami'an tsaron da ba sojoji ba na Iraqi a kusa da Nasiriyyah. Sojojin taron dangi suna ci gaba da taruwa a yankin domin kai farmaki kan babban birnin kasar.

XS
SM
MD
LG