A yau ne babbar kotun tarayyar Nigeriya zata yanke hukumci game da kararrakin da wasu jam'iyyu suka shigar game da babban zaben da za a fara daga Jibi Asabar.
Jam'iyyun NDP da UNPP ne suka shigar da kararrakin suna kalubalantar yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar ta tsara na gudanar da zabubbukan kasar. Ita dai jam'iyyar ta ce, hukumar ta karya wani sashi na dokar zaben kasar ta shekara ta 2002 tunda yake bata dakatar da aikin rubutawa, gyarawa da tantance sunayen masu zabe, kwanaki 60 kafin zaben ba. Don haka jam'iyyar ta NDP ta nemi kotu ta tilastawa hukumar ta INEC ta jingine zaben har sai ta yi hakan.
Ita kuwa jam'iyyar UNPP cewa ta yi, dokar zaben ta shekarar 2002 ta tanaji a baiwa kowane mai zabe katin zabe, amma har lokacin da jam'iyyar ta shigar da karar, kwanaki kalilan a fara a fara zaben, ba a fara bayar da katin zaben na ainihi ba. Don haka ita ma UNPP ta nemi kotu ta dakatar da zaben.
Kotun ta saurari hujjojin duka bangarorin a ranar Talatar data gabata kuma ta yi alkawarin bayar da hukumcinta a yau Alhamis.
A tattaunawar da ya yi da Sashin Hausa na VOA, babban sakataren hukumar zaben kasar ta Nigeriya, Dr. Hakeem Baba Ahmed ya ce, hukumarsa ta kammala dukkanin shirye-shiryen gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci, kuma cikin nasara. To amma hadakar wasu jam'iyyun adawa guda 17 sun bukaci hukumar ta INEC ta yi wa Nigeriya Kiyamul-Laili ta dakatar da zaben.
Shugaban Hadakar jam'iyyun, Malam Balarabe Musa na jam'iyyar PRP ya shedawa Sashin Hausa na VOA cewa zaben na iya haddasa tarzoma da tashin hankali a kasar ta Nigeriya.
A halin da ake ciki kuma masu zabe a wasu sassa na kasar ta Nigeriya suna guna-gunin cewa har yanzu ba su karbi katin zabensu ba, kwanaki biyu da fara aikin raba katin a kasar. Fiye da 'yan Nigeriya miliyan 60 ne suka cancanci jefa kuri'a a zaben da za a fara Jibi Asabar da na wakilan majalisun dokokin kasar, wanda daga shi sai na shugaban kasa da gwamnonin jihohi, wanda za a yi a ranar 19 ga wannan Wata na Afirilu.
An ce akasarin cibiyoyin da za a raba katunan duk a rufe suke.