Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Kunar-Bakin-Wake Ya Kashe Mutane Akalla 3 A Isra'ila - 2003-05-19


'Yan sandan Isra'ila sun ce wani bam da ya tashi a garin Afula dake arewacin kasar ya kashe mutane 4 ya raunata wasu mutanen su 30, wasunsu rauni mai tsanani.

Jami'ai suka ce maharin bam din ya tayar da wannan nakiya a lokacin da yake cikin layin binciken masu shiga wau kantuna. Suka ce watakila macen da aka kashe a wurin mai gadi ce, ba ita ce ta kai harin bam din kamar yadda aka zata da fari ba. Nan da nan 'yan sanda suka killace garin a bayan wannan hari.

Kungiyar 'yan kishin Falasdinu ta Islamic Jihad ta dauki alhakin kai wannan hari.

Wannan hari shine na biyar cikin kwanaki biyu. Tun farko a yau litinin, wani Bafalasdine dan kunar bakin wake dake tafiya kan keke ya tayar da bam kusa da jikin wata motar soja a zirin Gaza, ya raunata sojojin bani Yahudu uku a kusa da unguwar share-ka-zauna ta Yahudawa da ake kira Kfar Darom.

hare-hare na baya sun yi sanadin mutuwar 'yan Isra'ila su akalla tara. Hari mafi muni ya wakana jiya lahadi a birnin Qudus, a lokacin da wani dan kai hari da yayi shigar limaman Yahudawa ya tarwatsa kansa cikin wata motar fasinja, ya kashe 'yan Isra'ila 7.

Kungiyar 'yan kishin Falasdinu ta Hamas ta dauki alhakin kai dukkan hare-haren im ban da na baya-bayan nan.

Isra'ila ta rufe bakin iyakokinta da Yankin Yammacin kogin Jordan da Zirin Gaza a bayan harin na jiya lahadi. Firayim minista Ariel Sharon kuma ya jinkirta ziyarar da yayi niyyar kawowa nan Washington domin tattaunawa da Shugaba Bush a kan shirin Amurka na shimfida zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

XS
SM
MD
LG