Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Fiye da Dubu Daya Sun Mutu A Girgizar Kasa A Aljeriya - 2003-05-22


Kungiyoyin agaji sun ce suna namijin kokari tare da fatan samo mutane da ransu a karkashin gine-ginen da suka rushe a sanadin girgizar kasa mai tsananin karfi da ta ratsa arewacin kasar Aljeriya jiya laraba da daddare. Suka ce ya zuwa yanzu, an tabbatar da mutuwar mutane fiye da dubu daya a wannan girgizar kasa, yayin da kusan dubu 5 suka ji rauni, akasari a yankunan dake gabas da Algiers, babban birnin kasar.

Wakilin Muryar Amurka dake yankin Gabas ta Tsakiya, ya ambaci ma'aikatan agaji a Aljeriya suna fadin cewa suna fuskantar mawuyacin aiki na tono mutane daga karkashin kankare, da gine-ginen siminti na gidajen kwanan da suka rushe.

'Yan Aljeriya suka ce wasu jerin gidajen kwana sun yi ta faduwa kamar bunu a lokacin da kasa tayi motsi. A garin Boumerdes mai tazarar kilomita 50 a gabas da birnin Algiers, inda wannan girgiza ta fi yin barna, gine-gine kamar dozin guda suka rushe baki daya. Ana fargabar cewa akwai dubban mutane a binne a karkashin wadannan gine-gine.

Shugabar gamayyar kungiyoyin agajin Red Cross da Red Crescent a Afirka ta Arewa, Anne Le Clerc, ta ce tana tattaunawa a kai a kai da kungiyar agaji ta Red Crescent ta Aljeriya domin tura ma'aikata da kayan agajin da ake bukata.

Ta ce ma'aikatan agajin kungiyar Red Crescent ta Aljeriya sun kwana suna aikin ceto mutanen da gine-gine suka rusa musu a kai, suna kai su asibiti, suna taimakawa wajen tara gudumawar jini tare da kwantar da hankulan mutanen da suka firgita. Har yanzu suna ci gaba da wannan aiki, in ji ta.

Ms. Le Clerc ta ce katsewar wutar lantarki a ciki da kewayen birnin Algiers ta kara munin wannan lamari. Ma'aikatan kiwon lafiya sun ce asibitoci a babban birnin kasar da kuma garuruwan da girgizar kasar ta fi yi wa barna, kamar Rouiba, suna fuskantar matsananciyar wahala wajen kula da dubban mutanen da suka ji rauni.

Rahotanni daga lardin Boumerdes sun ce ana tattara gawarwaki a wajen asibitoci, yayin da ake jinyar mutanen da suka ji rauni a filin Allah.

Hukumomin Aljeriya sun roki likitoci da ma'aikatan jinya da su taimaka, yayin da su kuma sauran al'umma aka roke su da su kai gudumawa da jini.

Wannan girgizar kasa ta kai awu 6 da digo 7 a ma'aunin motsin kasa na Richter. Kasa ta sake yin motsi fiye da sau 200 a cikin sa'o'i biyu da girgizar kasar, kuma ana sa ran zata ci gaba da yi nan gaba.

Shugab aAbdel-Aziz Bouteflika na Aljeriya ya ziyarci wadanda suka ji rauni ya kuma yi rangadin yankunan da girgizar ta yi wa barna. Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce ana samar da tantuna da barguna da kuma janareta ga mutanen da suka firgita har ba zasu iya komawa cikin gidajensu ba. A jiya dai, mutane masu yawan gaske da suka firgita da yadda kasa ta ci gaba da yin motsi bayan girgizar ta farko sun kwana a waje a kan tituna ko a filayen shakatawa. Wasu kuwa, sun cika motoci da kayayyakinsu suka bar yankin baki daya.

XS
SM
MD
LG