Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al'ummar Kasar Rwanda Zasu Jefa Kuri'ar-Raba-Gardama Kan Sabon Tsarin Mulki - 2003-05-26


Al'ummar Rwanda suna jefa kuri'un raba-gardama kan sabon tsarin mulkin da zai yi kokarin karfafa mulkin dimokuradiyya tare da rigakafin kashe-kashen kare-dangin da aka yi a kasar shekaru 9 da suka shige.

Mutane kusan miliyan 4 da suka yi rajistar jefa kuri'a ne zasu iya kada kuri'unsu kan daftarin tsarin mulkin, wanda majalisar dokokin wucin-gadi ta Rwanda ta amince da shi a karshen watan Afrilu. Za a dauki kwanaki kafin a samu sakamakon wannan kuri'a.

Sabon tsarin mulkin yayi tanadin cewa shugaban kasa zai yi wa'adin shekaru 7 ne kan karagar mulki, sannan kuma an shimfida ka'idojin gudanar da ayyukan jam'iyyun siyasa.

Wannan kuri'ar raba-gardama ta yau litinin, tana zaman share-fagen zaben shugaban kasa da na majalisar dokoki na farko da za a yi a kasar Rwanda na jam'iyyu da dama a nan gaba cikin wannan shekara.

XS
SM
MD
LG