Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Na Amurka Zai Yi Tattaki Zuwa Gabas Ta Tsakiya - 2003-05-26


Ana sa ran shugaba Bush zai yi taron koli da firayim ministocin Isra'ila da Falasdinawa a can yankin Gabas ta Tsakiya, da yake yanzu majalisar zartaswar Isra'ila ta amince, bisa sharadi, da shirin da Amurka ta gabatar na cimma zaman lafiya da Falasdinawa.

Jami'an Isra'ila sun ce mai yiwuwa a gudanar da taron kolin cikin mako mai zuwa a Jordan, amma kuma ministan harkokin wajen Jordan, Marwan Muasher, ya ce har yanzu ba a yanke shawara a kan inda za a gudanar da taron ba.

Har ila yau kuma, jami'an Amurka sun ce tana yiwuwa shugaba Bush ya gana da shugabannin Misra, Jordan da Sa'udiyya, wadanda su ma suka goyi bayan shirin na samar da zaman lafiya.

Taron kolin da shugaban na Amurka zai yi da firayim minista Ariel Sharon na Isra'ila da Mahmoud Abbas na Falasdinu zai zo bayan ya halarci taron kolin tattalin arzikin da za a yi a farkon watan gobe na Yuni a Faransa.

XS
SM
MD
LG