Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Morocco Ta Ce Wanda Ya Kitsa Kai Hare-Haren Bam Ya Mutu A Gidan Wakafi - 2003-05-28


Wani lauyan gwamnati mai gabatar da a Morocco, ya ce hukumomi sun damke mutumin da ake zargin cewa shine ya kitsa munanan hare-haren bam da aka kai cikin wannan wata a birnin Casablanca, amma kuma mutumin ya mutu a lokacin da ake tsare da shi a gidan wakafi.

Mai gabatar da kararrakin ya ce wannan mutumi mai suna Abdelhaq Moulsebbat, ya mutu a sanadin cututtukan hanta da zuciya wadanda suka yi tsanani sosai.

Ya ce a ranar litinin aka kama Moulsebbat a birnin Fes dake tsakiyar Morocco, ya kuma mutu a lokacin da ake garzayawa da shi zuwa asibiti. Lauyan na gwamnati bai yi wani karin bayani game da shekarun mutumin ko kuma yana da alaka da wata kungiyar 'yan ta'adda ba.

Hare-haren bam din an Casablanca sun yi sanadin mutuwar mutane 43, cikinsu har da 'yan kunar-bakin-wake 12 da suka kai hare-haren.

XS
SM
MD
LG