Yanayi maras kyau ya tilastawa Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta Amurka, NASA, ta sake jinkirta harba wani kumbon da zai je ya binciko duniyar Mars.
A bayan da masana suka bayyana cewa hadarin ruwan sama ya doshi wurin da za a harba kumbon, sai hukumar NASA ta dage yin hakan har sai gobe talata da karfe 2 na rana (karfe 7 na maraice agogon Nijeriya).
Wannan kumbon zai tafi duniyar Mars dauke da wani mutum-mutimi na karfe mai suna "Rover" wanda zai gudanar da bincike ya ga ko ruwa ya taba zama a duniyar Mars na tsawon lokacin da halittu zasu iya rayuwa. Binciken da aka yi a can baya ya nuna cewa akwai wani lokaci a baya da duniyar Mars ke da ruwa.