Jami'an shawarwarin gwamnati da na 'yan tawayen Liberiya dake ganawa a kasar Ghana, sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar tsagaita wuta, wadda ta kunshi batutuwan da suka hada har da yin murabus din shugaba Charles Taylor.
Mashawarta a zauren taron na Ghana sun fada kafin bukin rattaba hannu a yau talata, cewar a karkashin wannan yarjejeniya, bangarorin zasu kafa gwamnatin rikon kwarya a Liberiya nan da kwanaki 30.
Suka ce Mr. Taylor ba zai shiga cikin wannan gwamnati ba.
Labarin kulla wannan yarjejeniya ya haddasa bukukuwa a titunan Monrovia, babban birnin Liberiya, wanda 'yan tawaye suka yi makonni biyu da yi wa kofar-rago.
Wannan yakin basasa na Liberiya ya samo asali shekaru hudu ad suka shige. Kungiyoyin 'yan tawaye biyu, LURD da MODEL, suna rike da kashi 2 cikin 3 na kasar.
An fara tattaunawar neman zaman lafiya cikin wannan wata a Akosombo a kasar Ghana, karkashin jagorancin kungiyar ECOWAS.