Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Mutane Sun Cunna Ma Kansu Wuta Yayin Da Iraniyawa Ke Zanga-Zanga A Turai - 2003-06-19


Wasu Iraniyawa uku sun bunka wa kawunansu wuta a wuraren zanga-zanga biyu a nahiyar Turai, inda ake nuna rashin jin dadin matakan da hukumomin kasar Faransa suka dauka na dira kan wata kungiyar 'yan adawar Iran.

Wasu mazaje biyu sun cunna ma kansu wuta a lokacin da wasu mutane su 20 suka yi zanga-zanga yau alhamis a kofar ofishin jakadancin Faransa dake birnin Rum a kasar Italiya.

Wani dan kasar ta Iran ma ya cinna ma kansa wuta a lokacin irin wannan zanga-zanga a Berne, babban birnin kasar Switzerland.

Hukumomi ba su ce ga halin da wadannan mutane uku suke ciki a yanzu haka ba.

Dukkansu suna zanga-zanga ce ta nuna rashin jin dadin matakan da Faransa ta dauka na kama Iraniyawa kimanin 160 na kungiyar adawar Iran din nan mai suna Mujahideen.

Amurka da Tarayyar Turai sun ayyana wannan kungiya a zaman ta 'yan ta'adda, haka kuma wani jami'in Faransa ya ce kungiyar ta shirya kai hare-hare kan ofisoshin jakadancin Iran dake Turai.

XS
SM
MD
LG