Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Harbi Sojan Amurka Yau A Bagadaza - 2003-06-27


An harbi wani sojan Amurka yau Jumma'a a Bagadaza, a hari na baya-bayan nan kan sojojin mamaya karkashin jagorancin Amurka da ke Iraqi.

Shaidu sun ce an harbi wannan soja a fuska, ko kuma a wuya, a lokacin da yake sayen faifayin bidiyo yau Jumma'a daga wanidan tireda na gefen hanya a wata unguwar arewa maso yammacin Bagadaza.

Maharbin ya tsere cikin jama'a a yayin da sauran sojojin Amurka suka garzaya da wannan soja zuwa asibiti. Jami'an ma'aikatar tsaron Amurka sun gaskata labarin harbin, amma ba su yi karin bayani kan halin da sojan yake ciki a yanzu ba.

Wannan harin ya zo a daidai lokacin da sojojin Amurka suke ci gaba da yin farauta ta sama da kuma ta kasa, suna neman wasu sojojin Amurka biyu da suka bata ranar alhamis da daddare a garin Balad dake arewa da Bagadaza. An bada rahoton bacewar sojojin biyu, bayan da suka kasa amsa kiraye-kirayen da aka yi ta yi musu ta wayar iska.

jami'an tsaron Amurka sun dora laifin wadannan hare-hare da ake kai musu kusan a kullum a kan abinda suka kira ragowar magoya bayan Saddam Hussein.

XS
SM
MD
LG