Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babban Jami'in Nukiliya Na Iran Yana Rasha - 2003-06-30


Babban jami'in nukiliya na kasar Iran yana birnin Moscow, domin tattaunawa da manyan jami'an gwamnatin Rasha, yayin da ake ci gaba da bayyana damuwar cewa Iran tana shirin kera makaman nukiliya a asirce.

Ana sa ran cewa babban jami'in makamashin nukiliya na Iran, Gholamreza Aghazadeh, da ministan harkokin wajen Rasha, Igor Ivanov, zasu gana a yau domin tattauna hadin kai a tsakanin kasashensu biyu.

Rasha tana taimakawa Iran wajen gina masana'antar samar da wutar lantarki daga nukiliya a birnin Bushehr mai tashar jiragen ruwa, duk da matsin lambar da Amurka take yi mata a kan ta daina.

Rasha ta yi kira ga Iran da ta kara ba da hadin kai ga sufetocin nukiliya na MDD. Iran ta ce ita shirinta na nukiliya na lumana ne.

XS
SM
MD
LG