Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bindige, Aka Kashe Magajin Garin Wani Birni A Iraqi - 2003-07-16


An kashe magajin garin wani birni a kasar Iraqi, bayan da wasu mutanen garin suka zarge shi da laifin hada kai da sojojin Amurka.

Rundunar sojojin Amurka ta tabbatar da cewa an bindige aka kashe magajin garin birnin Hadithah, Mohammed Nayil al-Jurayfi, yau laraba, lokacin da yake tafiya cikin motarsa a birnin. Har ila yau an kashe dan magajin garin a wannan hari.

Birnin Hadithah yana arewa maso yamma da Bagadaza, a wani yanki na Musulmi 'yan mazhabin Sunni wadanda suke yin gaba da mamaye kasar da sojoji suka yi karkashin jagorancin Amurka.

Gidan telebijin na al-Jazeera ya ce mutanen birnin suna zargin magajin garin da laifin yin aiki tare da Amurkawa.

Wannan kisa ya zo a wannan ranar da aka kai hare-hare dabam dabam kan sojojin Amurka a ciki da wajen Bagadaza. An kashe sojan Amurka daya, aka raunata wasu uku a lokacin da aka kai hari kan motocinsu a yammacin Bagadaza.

A wani harin dabam, an cilla makami mai linzami kan wani jirgin daukar kaya na soja dake kokarin sauka a filin jirgin saman Bagadaza, amma kuma bai sami jirgin ba.

An kai wadannan hare-hare a wannan ranar da ake cika shekaru 24 da kwace mulkin da Saddam Hussein yayi a Iraqi.

XS
SM
MD
LG