Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tony Blair Yana Kan Hanyar Zuwa Asiya - 2003-07-18


Firayim minista Tony Blair na Britaniya yana kan hanyarsa ta zuwa birnin Tokyo, babban birnin japan, domin fara ziyarar kasashen yankin Asiya, a bayan gajeruwar ziyarar da ya kawo nan Washington inda ya tattauna da shugaba Bush.

Ana sa ran tattaunawar da Mr. Blair zai yi da shugabannin kasashen Japan, da China da Koriya ta Kudu za ta mayar da hankali kan gardamar da ake yi game da shirin nukiliya na Koriya ta Arewa.

Har ila yau, an shirya firayim ministan na Britaniya zai yi tattaki zuwa tsibirin Hong Kong, wanda Britaniya ta yi wa mulkin mallaka, wanda kuma a yanzu ke fama da tabarbarewar tattalin arziki da zanga-zanga kan wata dokar haramta cin amanar kasa, wadda masu sukar lamiri suka ce tana barazana ga hakkin bil Adama.

XS
SM
MD
LG