Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya Na Nijeriya Sun Fara Sauka A Liberiya - 2003-08-04


Ayarin farko na sojojin kiyaye zaman lafiya na Afirka ta Yamma sun sauka a kasar Liberiya.

Helkwaftoci guda biyu, kowanne dauke da sojojin Nijeriya 20, sun sauka yau litinin cikin ruwan sama kamar da bakin kwarya a babban filin jirgin saman Monrovia.

Ana sa ran sojojin Nijeriya su 300 zasu sauka a kasar yau litinin a lokuta dabam-dabam. Wadannan sune sojojin share fage na rundunar kiyaye zaman lafiyar da zata kunshi dakaru fiye da dubu uku, ciki har da sojoji daga Ghana da Mali da Benin da kuma Togo.

Amurka ta yi alkawarin taimakawa rundunar da kudi da kayan aiki. Manufar tura wannan runduna ita ce dawwamar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Liberiya ta hanyar tabbatar da cewa ana yin aiki da shirin tsagaita wuta tare da taimakawa kungiyoyin agaji wajen rarraba abinci da ruwan sha da magunguna.

Watanni biyun da aka yi ana gwabza fada kusan babu tsayawa a tsakanin sojojin gwamnati da na 'yan tawayen Liberiya, ya ragargaza Monrovia. Mutane har dubu daya suka mutu a wannan fada, yayin da wasu daruruwan dubbai suka kwarara zuwa cikin babban birnin suna neman mafaka daga wannan fada. Da yawa suna kwana a kan tituna babu ruwan sha ko abinci ko wuraren ba-haya.

Jim kadan kafin sojojin kiyaye zaman lafiyar su sauka, babbar kungiyar 'yan tawayen Liberiya ta LURD ta ce zata janye daga wuraren da take rike da su a Monrovia da zarar sojojin sun isa can.

Shugaba Charles Taylor na Liberiya ya ce zai sauka daga kan mukaminsa a ranar 11 ga watan Agusta. Amma kuma Mr. Taylor bai fadi ranar da zai bar kasar zuwa Nijeriya ba, inda aka yi masa tayin mafaka, ya kuma karba.

XS
SM
MD
LG