Wani sanannen dan majalisar dattijan Amurka yayi kira ga Amurka da ta yi kokarin ganin Majalisar Dinkin Duniya ta zartas da sabon kuduri na neman karin taimakon kasashen duniya wajen sake gina kasar Iraqi.
Richard Lugar dan jam'iyyar Republican, kuma shugaban kwamitin hulda da kasashen waje a majalisar dattijan Amurka, ya fada a jiya lahadi cewar sabon kuduri daga Kwamitin Sulhun MDD zai kara jaddada halalcin sojojin mamayan da Amurka take yi wa jagoranci a Iraqi.
Mr. Lugar ya ce idan Kwamitin Sulhun ya amince da kuduri, kasashen da suka yi adawa da yaki a Iraqi zasu iya samun karfin guiwar shiga aikin sake gina kasar da ake yi a yanzu.
Faransa da Rasha da kuma Jamus, wadanda suka jagoranci yin adawa da kai wa Iraqi farmakin soja, sun nuna cewa zasu iya taimakawa a kokarin sake gina kasa idan har aka fadada rawar da MDD zata taka cikin wannan aikin.
Sanata Lugar ya ce ya kamata gwamnatin shugaba Bush ta zana kasafin kudin da zai bayyana yawan kudin da za a kashe wajen sake gina kasar Iraqi a cikin shekaru biyar masu zuwa.