Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijeriya Da Benin Zasu Sake Bude Bakin Iyakarsu A Yau Jumma'a - 2003-08-15


Shugabannin Nijeriya da Jamhuriyar Benin sun yarda zasu sake bude bakin iyakarsu a yau jumma'a.

Wannan labari yana kunshe cikin wata sanarwar da aka bayar a karshen ganawa tsakanin shugaba Olusegun Obasanjo na Nijeriya da takwaransa na Jamhuriyar Benin, Mathieu Kerekou. Shugabannin biyu sun gana a garin Badagry na kudu maso yammacin Nijeriya, mai tazarar kilomita 20 daga bakin iyakarsu.

A ranar asabar Nijeriya ta rufe bakin iyakar tasu mai tsawon kilomita 770, tana mai fadin cewa wannan yanki ya zamo muhimmiyar kafar satar fita da yara kanana, da fasa kwabrin makamai, da wasu ayyukan da suka sabawa doka. Nijeriya tana son Benin ta dauki tsauraran matakan murkushe aikata laifuffuka daga tsallaken iyaka.

Kafin wannan ganawa ta su, shugaba Kerekou na Jamhuriyar Benin yayi na'am da cewa akwai wannan matsala ta masu tsallakawa Nijeriya suna aikata laifi su gudo, ya kuma yi alkawarin yin aiki tare da Nijeriya wajen murkushe wannan.

Kwararru sun yi kashedin cewa dukkan kasashen biyu za su fuskanci matsalar tattalin arziki idan aka ci gaba da rufe bakin iyakar, amma kuma Jamhuriyar Benin zata fi jin jiki fiye da babbar makwabciyar tata.

XS
SM
MD
LG