Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fadan Kabilanci Ya Barke A Yankin Niger Delta Na Kudancin Nijeriya - 2003-08-17


Fadan kabilanci ya barke a yankin makwararin ruwan kogin Kwara mai arzikin mai a kudancin Nijeriya, abinda ya sa ala tilas hukumomi suka kafa dokar hana yawon dare.

Shaidu sun ce mutane akalla uku suka mutu a tashin hankalin da aka yi Jumma'a da asabar a garin warri mai tashar jiragen ruwa. Wasu rahotannin sun ce mutane har 20 ne suka mutu. An lalata gidaje akalla 30 a wannan fada.

Rahotanni daga yankin sun ce wannan fada shine mafi muni da aka gwabza tun watan Maris a tsakanin 'yan kabilun Itsekiri da Ijaw mazauna wannan wuri. A fadan na baya an kashe mutane masu yawa har ala tilas manyan kamfanonin mai na kasa da kasa suka rage ayyukansu da wajen kashi 40 daga cikin 100.

Ana zaman tankiya mai muni a tsakanin kabilun Ijaw da Itsekiri, inda ake samun rahotannin barkewar fada a kai a kai a tsakaninsu. Gasar neman cin moriyar arzikin man fetur na yankin ita ce ke tayar da wannan fada a lokuta da dama.

XS
SM
MD
LG