Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ci Gaba Da Gwabza Fada A Yankin Niger Delta Na Kudancin Nijeriya - 2003-08-18


'Yan bangar kailun da ba su ga-maciji da juna sun gwabza jiya lahadi a birnin Warri mai tashar jiragen ruwa, a rana ta uku a jere da wadannan 'yan ta-kifen ke bai wa hammata iska a yankin makwararin ruwan kogin kwara.

Hukumomi ba su bayyana adadin wadanda aka kashe a wannan fada tsakanin 'yan kabilar Ijaw da Itsekiri ba. Amma kamfanin dillancin labaran AP ya ce an kashe mutane fiye da 20 tun lokacin da aka fara gwabzawa a ranar Jumma'a.

'Yan ta-kife dauke da muggan makamai sun yi dauki-ba-dadi da dakarun tsaron dake kokarin maido da kwanciyar hankali, tare da tabbatar da cewa ana yin aiki da dokar hana yawon dare.

Daruruwan mutane sun mutu cikin 'yan shekarun nan yayin da aka gurgunta aikin tonon man fetur mai matukar muhimmanci ga tattalin arzikin Nijeriya a saboda fada tsakanin 'yan kabilun na Ijaw da Itsekiri.

Ba a san musabbabin barkewar wannan sabon fada ba, amma kuma a can baya kabilun biyu sun sha gwabzawa a dalilin neman kason arzikin man fetur. Haka kuma, su kan kai ruwa rani a saboda dalilan siyasa da rikici kan filaye.

XS
SM
MD
LG