Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Da Nelson Mandela Suna Kokarin Dinke Barakarsu - 2003-08-18


A bisa dukkan alamun da ake gani, shugaba Bush da tsohon shugaban Afirka ta Kudu mai farin jini, Nelson Mandela, suna kokarin kyautata dangantakarsu da ta sukurkuce.

Wani kakakin fadar White House ya ce a ranar asabar, Mr. Mandela ya bugo waya ma shugaba Bush, kuma daga cikin abubuwan da mutanen biyu suka tattauna har da kokarin yaki da annobar cutar kanjamau ta AIDS ko SIDA.

Mr. Bush ya amsa wannan waya ta Mr. Mandela a lokacin da yake ci gaba da hutunsa na wata guda a gidan gonarsa dake garin Crawford a Jihar Texas.

Mr. Mandela yana sahun gaba cikin masu yin Allah wadarai da yakin da Amurka ta jagoranci kaiwa kan kasar Iraqi, har ma akwai lokacin da ya bayyana shugaba Bush da maras kan gado ne. Mutanen biyu ba su gana ba a lokacin da shugaba Bush ay ziyarci Afirka ta Kudu a watan da ya shige.

XS
SM
MD
LG