Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hamas Ta Cilla Rokoki Kan Isra'ila - 2003-08-22


Masu zazzafan kishin Falasdinu na kungiyar Hamas sun cilla rokoki hudu zuwa cikin kudancin Isra'ila daga zirin Gaza, a bayan da suka lashi takobin daukar fansa mai tsanani ta kashe wani babban shugaban kungiyar da Isra'ila ta yi jiya alhamis.

Rundunar sojojin Isra'ila ta ce biyu daga cikin rokokin sun fada kan garin Sderot, suka lalata wani gida tare da raunata mutane da dama.

A halin da ake ciki, tankokin yaki na Isra'ila sun kutsa cikin garin Jenin a yammacin kogin Jordan cikin daren alhamisar nan a wani mataki na farautar masu kishin Falasdinu.

Wani rahoto ya ce an goce da harbe-harbe a tsakanin sojojin Isra'ila da Falasdinawa a Jenin. Ba a samu karin bayani ba.

Kungiyar Hamas da takwarorinta masu zazzafan kishin Falasdinu na kungiyar Islamic Jihad sun lashi takobin dauko fansar kisan babban jami'in Hamas, Isma'il Abu-Shanab, wanda aka kashe tare da wasu dogarawansa biyu a lokacin da wani jirgin helkwafta na sojojin Isra'ila ya cilla musu makami mai linzami a wata unguwa a Gaza.

Ana daukar wannan farmaki an isra'ila a zaman martanin harin kunar-bakin-wake da aka kai kan wata motar safa ranar talata a Qudus, inda aka kashe mutane 20.

Amurka ta ja kunnen bangarorin biyu da kada su yi watsi da shirin wanzar da zaman lafiya.

XS
SM
MD
LG