Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Ciniki Ta Duniya Ta Kulla Yarjejeniyar Samar Da Magunguna Masu Arha Ga Kasashe Masu Tasowa - 2003-08-29


Hukumar Ciniki ta Duniya, WTO, ta yarda da wata yarjejeniyar samar da magunguna masu araha ga kasashe masu tasowa domin su yaki kanjamau, zazzabin maleriya da wasu cututtukan.

Wakilan hukumar ta WTO sun cimma wannan daidaiton ra'ayi da maraicen alhamis a Geneva, a bayan da mashawarta daga Amurka, Indiya, Brazil, Afirka ta Kudu da Kenya suka daidaita kan wannan shiri kwana guda kafin wannan lokaci.

A yanzu babbar majalisar hukumar mai wakilai 146 zata tattauna ta zartas da shirin kafin ya fara aiki.

Yarjejeniyar zata kawo karshen jinkirin shekaru biyu da aka samu wajen zartas da wannan mataki wanda aka tsara da nufin samarwa da kasashe matalauta kwafen magunguna masu araha da zasu maye gurbin na magunguna ainihi na kamfanonin da suka kirkiro da su.

XS
SM
MD
LG