Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Faransa Da Jamus Sun Ce Akwai Bukatar Bai Wa MDD Muhimmiyar Rawa A Iraqi - 2003-08-29


Jamus da Faransa sun ce suna goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya ta taka muhimmiyar rawa a kasar Iraqi, amma kuma ba a san ko shawarar da gwamnatin Amurka ta gabatar yana iya samun goyon bayan majalisar ba.

Wazirin Jamus, Gerhard Schroeder, ya ce abu mafi alheri ga kasashen duniya ne su taimaka wajen tabbatar da kwanciyar hankali a Iraqi. Amma kuma ya ce Jamus ba ta da shirin tura sojojinta a cikin duk wata runduna ta kasa da kasa.

Tun da fari, ministan harkokin wajen Faransa, Dominique de Villepin, ya ce fadada rundunar sojan dake can a karkashin jagorancin Amurka kawai, ba shine zai biya bukata ba. Faransa ta ce ba zata tura sojojinta zuwa Faransa ba sai fa idan MDD ce zata jagoranci wannan runduna.

Babu daya daga cikin mutanen biyu da yayi furuci kan shawarar da Amurka ta gabatar cewar a kafa rundunar soja ta kasa da kasa wadda MDD zata amince da ita a kuma nada wani janar na sojan Amurka ya jagorance ta.

XS
SM
MD
LG