Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Ta Kare Matakan Da Take Dauka Game da Cutar Kanjamau Ta AIDS - 2003-09-05


China ta kare irin kwazon da ta nuna wajen yaki da cutar kanjamau ta AIDS, tana mai cewa babu kan gado a sukar da wata kungiyar kare hakkin bil Adama ta yi mata.

Wani kakakin ma'aikatar harkokin wajen China ya fada jiya alhamis cewa gwamnati tana bayar da himma wajen yin rigakafi da kuma kula da lafiyar wadanda suka kamu da cutar ta kanjamau.

Ya ce babu gaskiya a cikin duk wani zargin da ya musanta wannan ikirari nasa.

Kwana guda kafin wannan, kungiyar kare hakkin bil Adama ta "Human Rights Watch" mai hedkwata a birnin New York, ta bayar da rahoton dake cewa mutane da yawa masu fama da cutar kanjamau a China ba su samu magani a saboda asibitocin suna kin karbar su.

Rahoton ya ce a mafi yawancin lokuta ana mayar da masu fama da cutar kanjamau saniyar ware a China, ana kuma musuguna musu.

XS
SM
MD
LG