Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnati Da 'Yan Tawayen Sudan Sun Fara Tattaunawa - 2003-09-06


Madugun 'yan tawayen Sudan da wani babban jami'in gwamnatin kasar sun ci gaba da tattaunawa jiya Jumma'a a Kenya, inda suke fuskantar matsin lamba a kan su cimma yarjejeniyar kawo karshen yakin basasar shekaru 20 a kasarsu.

John garang, madugun 'yan tawayen kungiyar SPLA da mataimakin shugaban kasar Sudan, Ali Osman Mohammed Taha, sun yi ganawar farko ranar alhamis da maraice a garin Naivasha. Dukkansu sun bayyana kwarin guiwar wannan tattaunawa.

Jami'in kasar Kenya mai shiga tsakani a tattaunawar, tsohon janar na soja Lazaro Sumbeiyo, ya ce dukkan sassan suna fuskantar matsin lamba a kan su daidaita, ya kuma yi hasashen cewa za a cimma yarjejeniya nan da karshen wannan wata.

Tattaunawar neman zaman lafiya tsakanin 'yan tawaye da gwamnatin Sudan ta gamu da matsaloli cikin 'yan watannin nan a saboda wasu batutuwa, ciki har da yadda za a raba iko, da raba arzikin mai, a bayan gagarumar yarjejeniyar da suka kulla cikin shekarar 2000 a garin Menchako na Kenya.

A karkashin yarjejeniyar, an bai wa kudancin Sudan ikon zaben cin gashin kai a bayan shekaru shida.

XS
SM
MD
LG