Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya Sun Shirya Shiga Tsakiyar Kasar Liberiya - 2003-09-08


Sojojin kiyaye zaman lafiya na Afirka ta Yamma suna shirin shiga yankunan karkara na Liberiyainda ake fama da matsalar rashin bin doka da oda, a bayan jinkirin da aka samu daga gwamnatin kasar.

Ministan tsaron Liberiya, Daniel Chea, ya shaidawa Muryar Amurka cewa an kawar da matsalar da ta kawo jinkirin tura sojojin. Ya ce a yau litinin sojojin kiyaye zaman lafiyar zasu isa garin Kakata, a bayan da aka dage tafiyarsu can ranar asabar.

jami'an kiyaye zaman lafiya suka ce an jinkirta tafiyar sojojin domin a bai wa sojojin sa kai masu goyon bayan gwamnati lokaci na janyewa daga babbar hanyar motar da ta tashi daga Monrovia zuwa tsakiyar kasar.

An bayar da rahoton cewa sojojin 'yan tawaye suna kai hare-hare kan fararen hula a tsakiyar Liberiya, inda suka kori dubban mutane daga gidaje da kuma sansanonin 'yan gudun hijira. An ci gaba da gwabzawa a can, duk da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma tsakanin gwamnati da 'yan tawayen kusan makonni ukun da suka shige.

Sansanin da sojojin kiyaye zaman lafiyar zasu kafa a Kakata, zai zamo na farko a wajen birnin Monrovia tun a farkon watan Agusta lokacin da suka fara isa kasar da yaki ya lalata.

XS
SM
MD
LG