Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya Sun Isa Bayangarin Birni Na Biyu Wajen Girma A Liberiya - 2003-09-14


Sojojin kiyaye zaman lafiya na Afirka ta yamma suna bayangarin birnin Buchanan mai tashar jiragen ruwa dake bakin gabar kudu maso gabashin Liberiya, yayin da suke ci gaba da shiga sassan wannan kasa da yaki ya lalata.

Sojoji 550 daga Nijeriya da Benin da Togo sun shiga motoci suka doshi birnin na biyu wajen girma a Liberiya. Mutanen kauyukan dake kan hanya sun fito cike da murna suna jinjinawa sojojin.

A yau lahadi ake sa ran sojojin za su amshi ragamar wannan birni da 'yan tawaye suke rike da shi.

A watan da ya shige gwamnatin Liberiya da kungiyoyin 'yan tawaye biyu na kasar suka cimma yarjejeniyar zaman lafiyar da ta hada har da saukar shugaba Charles taylor daga kan mulki tare da girka sojojin kiyaye zaman lafiyar na Afirka ta Yamma.

An yi kusan shekaru 14 ana gwabza yakin basasa a Liberiya.

XS
SM
MD
LG