Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta ce zata sake nazarin dabarunta na gwabzawa da makaman nukiliya idan har kungiyar kawancen tsaron kasashen yammaci ta NATO ta ci gaba da abinda ma'aikatar ta kira kawancen tsokanar fada.
Wani rahoton da aka bayar jiya alhamis bai bayyana matakan da fadar Kremlin ta shugaban Rasha zata dauka ba, amma kuma ya ja kunnen NATO da ta kawo karshen manufofinta na nuna kiyayya ga Rasha.
Ministan tsaro Sergei Ivanov ya shaidawa jami'an soja cewa Rasha tana da 'yancin kai farmakin soja na rigakafi idan har aka yi barazana ga muradunta.
Shugaba Vladimir Putin ya shaidawa jami'an cewa Rasha tana da manyan rokokin kai farmaki masu yawa wadanda zasu iya daukar kundojin nukiliya, wadanda kuma za su iya ratsa kowace irin garkuwar makamai masu linzami da za a kafa domin tare su.