Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Tawagar MDD Zata Nazarci Batun Tsaro A Kasar Afghanistan - 2003-10-07


Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ya bayar da sanarwar shirye-shiryen tura wata tawaga zuwa Afghanistan domin nazarin hanyoyin kyautata tsaro a kasar.

Tawagar zata ziyarci Afghanistan daga ranar 31 ga watan Oktoba zuwa ranar 8 ga watan nuwamba.

Wasu mutanen da ake jin cewa 'yan tawayen Taleban ne su na kara kai hare-hare a cikin shekaru biyu a bayan da sojojin da Amurka ta yi wa jagoranci suka kori 'yan Taleban daga kan karagar mulki.

Har ila yau Kwamitin Sulhun ya ce wannan tawaga za ta kalli ayyukan kiyaye zaman lafiyar da kungiyar kawancen tsaro ta NATO take gudanarwa a Afghanistan. A jiya litinin, ma'aikatan jakadanci an NATO suka ce kungiyar ta yarda zata fadada ayyukanta na tsaro a Afghanistan zuwa wasu sassan kasar a bayan birnin Kabul.

XS
SM
MD
LG