Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Asusun 'Global Fund' Zai Bayar Da Agajin Dala Miliyan 623 Ga Wasu Kasashe - 2003-10-17


Wani asusun kasa da kasa da aka kafa domin yakar cututtukan kanjamau da zazzabin cizon sauro da kuma tarin fuka, ya amince da shirin bayar da gudumawar dala miliyan 623 ga kasashen dake yaki da wadannan cututtuka uku.

Wannan asusu mai suna "Global Fund" ya bayar da sanarwar cewa za a yi amfani da kashi 60 daga cikin 100 na wannan kudi domin yakar cutar kanjamau, akasari a nahiyar Afirka.

Majalisar zartaswar asusun na Global Fund dake ganawa jiya alhamis a kasar Thailand, ta ce za a yi amfani da kudin wajen samar da magungunan yakar hayayyafar kwayoyin halittar cuta dake iya tsawaita ran masu fama da kanjamau ga mutane dubu 200 masu wannan cuta a cikin shekaru biyun dake tafe.

Wannan sabuwar gudumawa ta sanya adadin kudin da aka ware domin gudanar da irin wannan aiki a yanzu ya kai dala miliyan dubu biyu da 100 a cikin shekaru biyu. An yi alkawarin bayar da dala miliyan dubu hudu da 700 ga wannan asusu. Ya zuwa yanzu, an amince da gudanar da shirye-shirye dabam-dabam a kasashe 125.

An kaddamar da asusun Global Fund shekaru biyu da suka shige tare da goyon bayan babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan.

XS
SM
MD
LG