Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Bin Kadin Laifuffukan Yaki Ta Tuhumi Hafsoshin Sojan Serbia Su Hudu - 2003-10-21


Kotun bin kadin laifuffukan yaki ta MDD ta tuhumi wasu janar-janar na sojan serbia su hudu, cikinsu har da babban jami'in tsaron al'ummar kasa na yanzu, da aikata laifuffukan yaki a yankin Kosovo cikin shekarun 1990.

Takardar tuhumar ta ambaci sunayen shugaban hukumar tsaron al'ummar kasa na Jamhuriyar serbia da Montenegro na yanzu, Janar Sreten Lukic, da wasu tsoffin hafsoshin sojan Yugoslaviya su uku.

Ana tuhumarsu da laifin shiryawa tare da bayar da umurnin korar karfi da yaji, da cin zarafi tare da kashe wasu daga cikin fararen hula 'yan kabilar Albaniyawa su dubu 800 daga yankin Kosovo a shekarun 1998 da 1999.

Masu gabatar da kararraki suka ce ko da yake wadannan janar-janar na soja ba su kashe kowa da hannunsu ba, haka kuma ba su kori fararen hula da kansu daga gidajensu ba, sune suke da alhakin laifuffukan da sojojin dake karkashinsu suka aikata.

XS
SM
MD
LG