Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Yau Jumma'a 'Yan Mauritaniya Zasu Zabi Sabon Shugaban Kasa - 2003-11-07


A yau Jumma'a al'ummar kasar mauritaniya za su zabi sabon shugaban kasa daga cikin 'yan takara shida, cikinsu har da shugaban kasar na yanzu da kuma wani tsohon shugaba.

Shugaba Maaouiya Ould Sid' Ahmed Taya, wanda yake takara a karo na uku, zai fuskanci tsohon shugaban kasar, Mohammed Ould Haidallah, da wasu 'yan takara hudu.

A jiya alhamis, hukumomi sun tsare Ould Haidallah, babban mai hamayya da shugaban, daga baya kuma suka sako shi a bayan da suka tuhume shi da laifin kulla makarkashiyar juyin mulki.

Mai gabatar da kararraki na gwamnati ya ce yana da bayanin cewa Ould haidallah da mukarrabansa sun shirya hambarar da gwamnati idan har bai ci zaben ba.

An kama Ould Haidallah tare da wasu mukarrabansa su biyar. Ba a san halin da mukarraban nasa suke ciki ba. A bayan da aka sako shi a jiya alhamis, Ould Haidallah ya ce zai yi na'am da sakamakon zaben idan har an gudanar da shi tsakani da Allah.

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun soki lamirin gwamnatin mauritaniya a saboda cin zarafin 'yan hamayya a lokacin yakin neman zabe. 'Yan kallo na kasashen waje sun ce ba su tsammanin za a gudanar da zaben shugaban kasar ba tare da ha'inci ba.

A ranar laraba, 'yan sandan kwantar da tarzoma sun yi amfani da barkonon tsohuwa domin hana 'yan hamayya yin maci a Nouakchott, babban birnin kasar. Mutane kimanin dubu daya ciki har da mata da yara sun taru domin nuna rashin jin dadin sumamen da aka kai wa Ould Haidallah da iyalansa.

Ould Haidallah yayi mulkin Mauritaniya na tsawon shekaru uku a bayan da ya kwace mulki a 1980. Shugaban kasar na yanzu shi ne yayi masa juyin mulki a 1984.

XS
SM
MD
LG