Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Koriya Ta Arewa Sun Yarda Zasu Sake Tattaunawa - 2003-11-12


Wani rahoton da aka wallafa ya ce Amurka da Koriya ta Arewa sun yarda za su shiga cikin wani sabon zagayen tattaunawa kan batun nukiliya cikin wata mai zuwa a birnin Beijing.

Jaridar "Asahi Shimbun" da ake bugawa kullum a kasar Japan ta bayar da rahoto a yau laraba cewa za a gudanar da taron kasashe 6 kan cijewar da ake fuskanta daga ranar 10 zuwa 13 ga watan disamba idan har jami'an jakadancin China suka shawo kan sauran kasashen suka yarda da wadannan ranaku.

A jiya talata wani kakakin ma'aikatar harkokin wajen China ya ce za a gudanar da tattaunawar nan ba da jimawa ba idan har a cewarsa komai ya tafi daidai, aka kuma samu nasarar kawar da wasu bambance-bamancen ra'ayi. Bai yi karin bayani ba.

A ranar litinin, mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka, james Kelly, ya ce watakila za a gudanar da tattaunawar a Disamba, amma yayi kashedin cewa har yanzu kasashen da abin ya shafa suna bukatar tsara wasu abubuwan.

tattaunawar tana mayar da hankali kan shirin kera makaman nukiliya na Koriya ta Arewa, wanda kasashen yankin da kuma Amurka suka kosa su ga an dakatar da shi. Babu wani ci gaban da aka samu a tattaunawar farko da aka yi cikin watan Agusta a tsakanin kasashen China da Amurka da kasashen Koriya biyu da Japan da kuma Rasha.

XS
SM
MD
LG