Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Adawa Sun Yi Kiran Da A Tayarwa Da Gwamnati Kayar Baya A Kasar Georgia - 2003-11-17


'Yan adawar kasar Georgia sun yi kiran da a kaddamar da wani gangami na kasa baki daya, na tayarwa da gwamnati kayar baya domin tilastawa shugaba Eduard Shevardnadze yayi murabus a saboda zaben 'yan majalisar dokoki da ake gardama a kai.

Madugun 'yan adawa Mikhail Saakashvili ya yi kiran da a rufe ofisoshin gwamnati da makarantu. Har ila yau yayi kira ga jama'a da su ringa busa kahon motocinsu, su kuma ki biyan haraji da wasu kudaden da gwamnati ke karba.

Shugaba Shevardnadze yayi gargadin cewa kiran nakkasa al'amura a kasar ya sabawa doka. Ya ce idan har 'yan adawar ba su janye wannan kira nasu ba, hukumomi zasu yi amfani da karfin dokokin kasar sosai a kansu.

'Yan kallo na kasashen waje sun ce an tabka magudi a zaben da aka yi makonni biyun da suka shige. An dakatar da kidaya kuri'u a yayin da kotuna ke sauraron zarge-zargen da 'yan adawa suka yi. Jam'iyyar dake goyon bayan gwamnati ita ce ke gaba da 'yar karamar tazara a sakamakon farko da aka samu.

XS
SM
MD
LG