Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka na marhaban da kokarin Nigeria na shirin tattaunawar zaman lafiya game da rikicin Darfur - 2004-08-13


A yau Alhamis Amurka ta yi marhaban da shirin da Nigeria ke yi na karbar bakuncin tattaunawar zaman lafiyar da za’a gudanar ranar 23 ga wannan wata na Agustan da muke ciki tsakanin jami’an gwamnatin Sudan da kuma shugabanin ‘yan tawayen Darfur. Shugaban Nigeria Chief Olusegun Obasanjo ne zai jagoranci taron a Abuja babban birnin tarayyar kasar. Har ila yau, Amurkan ta karyata da kakkausan-harshe, zargin da gwamnatin Sudan din tayi na cewar wai makasudin da yasa kasashen yammacin duniya ke katsalandan cikin matsalar Darfur duk be wuce kwadayinsu na samun damar handame albarkatun man-fetur din da Sudan ke da shi ba.

Ita Amurka dai tun ba yau ba ta ke wa’azin cewa, babbar hanyar da za’a bi domin warware rikicin na Darfur ta ta’allaka ne da kawo karshen matsalar jinkan da yankin ke fama da shi. A wani dan jawabin da mukaddashin kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka Mr. Adam Ereli ya yi ya bayyana cewa, shi wannan kokari da Nigeria ke yi, wanda kuma dukkan bangarorin biyu masu rigima da juna suka yadda da shi “na da muhimmancin gaske kuma wani ci gaba ne da muke marhaban da shi’.

Amma Mr. Ereli ya kara da cewa, “Ya zama waji a bi duddugin wannan matsala, kuma a sanya bangarorin biyu dake rigimar su zauna domin tattaunawa da juna. Har ila yau, lallai ne gwamnatin Sudan ta dauki matakan kare rayukan al’ummarta da kuma shiga wata tattaunawa da niyyar sulhunta ban-bancen siyar da ke tsakaninta da ‘yan tawayen.

A wani bangaren kuma, Shugaban Sudan Omar al-Bashir ya yi wani jawabi yau Alahamis a birnin Khartoum inda ya bayyana zarginsa ga kasashen yammacin duniya game da makasudinsu na hakika kan rikicin Darfur. Shi dai a ganinsa, duk bai wuce ganin cewa sun tayar-da-zaune-tsaye ba ne a kasar ta Sudan, domin su sami damar babakere kan albarkatunta na gwal da kuma man fetur.

Gwamnatin Amurka ta musanta wannan zargi a fusace inda ta kuma ba da martani ta hanyar kakin ma’aikatar harkokin kasashen wajenta Mr. Erili wanda ya ce, “Wannan ba batun maganar fetur ko gwal ba ce. Wannan batu ne da ya shafi kokarin tswamo al’ummar Sudan daga masibun cututtuka, yinwa, fyade da kuma kisan-gilla. Wannan shine halin da mutanen Darfur su ke ciki. Kuma shi ya sa mu kai ruwa-mu-kai-tsaki a cikin al’amarin. Saboda haka kuma al’ummar kasa-da-kasa ke magana da murya daya don bukatar ganin gwamnatin Sudan ta duki kwakwaran mataki, kuma na zahirn da kowa zai gani ya kuma shaida”. Ita kuwa Majalisar Dinkin Duniya ta siffanta rikicin Darfur a matsayin matsalar jinkai mafi munin da duniya ke fuskanta a halin yanzu. A sakamakon wannan matsala dai tuni mutane 50,000 sun rasa rayukansu, an kuma tursasawa fiye da milyan daya barin gidajensu har sai da su ka sami mafaka a sansanon ‘yan gudun hijira da ke Darfur da makociyarta Chadi.

XS
SM
MD
LG