Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mabiya Shi'a sun taru a masallacin Najaf  - 2004-08-27


Mabiya Shi'a sun taru a masallacin Najaf bayan yarjejeniyar zaman lafiya

Dubannin musulmi mabiya darikar Shi'a sun taru a masallacin sayyidina Ali dake birnin Najaf abin da ake gani ya kawo karshe na hakika a fadan sati uku. Dubannin maziyarta sun yi cincirindo a masallacin don yin sallar juma'a suna kabara suna kuma buka kirjinsu. An rika sa sakon Moqtadqa al-Sadr ta lasifikar masallacin wanda ke umartar mabiyansa ba kawai su bar masallacin ba ,a'a su bar ma gaba daya biranen Najaf da Kufa. Biranen biyu sun kasance fagen kazamin fadace -fadace a cikin makwanni, a inda mayakan al-Sadr suke amfani da masallacin a matsayin dandalin shirya ayyukansu. Amma a ranar alhamis ya amince da shirin zaman lafiya wanda babban shugaban mabiya Shi'a Ayatullahi Ali Sistani ya gabatar. Ayatullahin ya komo Najaf bayan zaman jiyya na mako uku a Ingila da kuma komowarsa ne ya fara tattaunawa da al -Sadr A tsarinsa Najaf da Kufa za su kasance inda babu amfani da makamai kuma za a janye dukkanin sojojin kasashen waje daga birane masu tsarki a bar tsaronsu a hannun 'yan sandan Iraqi.Ya kuma yi kira da a biya diyya ga wadanda suka tagayyara sakamakon wannan rikici. A ranar Juma'a, yan jaridu sunce sun ga amalanke cike da bindigogi da rokoki ana fitar dasu daga ckin masallacin. 'Yan sanda sun rika caje masu fita daga cikin masallacin kuma sun samu akasarinsu basa dauke da makamai. Sojojin Amurka sun kasance a wurarensu zagaye da masallacin amma an dakatar da harbe-harbe. Awanni arba'in da takwas a baya, masallacin ya kasaance fagen gabzawa tsakanin sojojin Amurka da kuma magoya bayan al-Sadr. A wata sabuwa kuma, gidan talabijin na al-Jazira yace yana da hoton bidiyo wanda ke nuna kashe dan jaridar kasar Italiya. Dan jaridar,Enzo Baldoni ya bace a makon da ya wuce akan hanyarsa ta zuwa Najaf daga Baghdad. Wata kungiya mai kiran kanta 'Sojojin Musulunci' daga baya sun nuna bidiyon da suke rike da shi. Kungiyar bata yi barazanar kashe shi ba amma tace ba zata iya tabbatar da tsaron lafiyarsa ba muddin Italiya bata janye sojojinta kimanin dubu uku daga Iraqi ba. A makon da ya wuce ne kungiyoyin kwallon kafa na kasashen Italiya dana Iraqi aka shirya zasu yi wasa a a gasar olympics a can Athens.Dukkanin kungiyoyin sun yarda su daura bakin kyalle don girmama Baldoni.

XS
SM
MD
LG