Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron samar da zaman lafiya a Sudan zai ci gaba - 2004-08-30


Ana sa ran taron samar da zaman lafiya a Sudan ya shiga mako na biyu a Najeriya bayan dan bata lokaci da ka samu wanda ya hada da kauracewa taron daga bangaren 'yan tawaye don yin zaman makokin farar hula da suka yi zargin sojojin gwamnati sun kashe musu.

Wakilan gwamnatin Sudan da bangarorin yan tawaye biyu suna tattaunawa kan abubuwa masu sarkakiya musamman wanda suka shafi maganar kwance damarar makamai da kuma harkar bada agaji ga mutanen da suka rasa matsuguni a ckin kasar.

Shugaban daya daga cikin bangaren 'yan tawen, na kungiyar SLMA, Mohammed Ahmed al-Nur ya yi kashedi ga gwamnatin Sudan kan ta tsayar da rikicin Darfur muddin tana so a samu nasara kan tattaunawar zaman lafiyan da ake yi.

'Ba zamu sake zuwa irin wadannan tattaunawar zaman lafiya ba idan gwamnatin Sudan bata daina karya yarjejeniyar tsaida buda wuta ba, kuma har yanzu bata mutunta 'yancin dan Adam a zahiri', ya jaddada. 'Gwamnatin da ya kamata ta kare rayukan farar hula itace take kai musu hari ba tare da mutunta yancinsu ba.'

Bangarorin 'yan tawaye suna zargin bangaren dakarun Janjaweed dana gwamnati da karya yarjejeniyar samar da zaman lafiya bayan da suka kashe fararen hula da dama a 'Yankin Darfur a yammacin Sudan a makon jiya.

Kungiyar hada kan kasashen Afirka ta AU wadda ke shugabantar taron tattaunawar a Abuja tana bincikar wannan zargin kuma tace masu sa idonta a Sudan zasu aiko da rahotansu a cikin wannan makon.

Sabuwar rundunar sojoji dari sun bar Najeriya a litinin dinnan don haduwa da rundunar tabbatar da tsaro ga jami'an tabbatar da tsayar da buda wuta na kungiyar AU a 'yankin Darfur.

Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya a halin yanzu yana nazarin rikicin kasar Sudan domin yanke shawara kan irin matakin da ya kamata ya dauka.Kwamitin tsaron yayi barazanar azawa gwamnatin Sudan takunkumi muddin bata tsayar da rikicinba ya zuwa karshen watan Agusta.

XS
SM
MD
LG