Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani bum da ya tashi a Fallujah ya kashe sojin  Amurka bakwai... - 2004-09-06


Wani bum da ya tashi a Fallujah ya kashe sojin Amurka 7 da wasu masu gadi ukku 'yan Iraqi. Sojin Amurka sun ce wani bum da ya tashi daga cikin wata mota ya kashe sojojin kundunbalar Amurka bakwai da wasu masu tsaron kasa 'yan Iraqi a cikin wani ayarin motar soji a wajen birnin fallujah.

Wannan mumunar tashin bum din ya kachachala motocin sojin Amurka guda biyu. Harin bum din, shi ne mafi muni da aka kai wa sojin na Amurka a cikin watanni da dama.

Fallujah dai wuri ne inda masu gwagwarmaya 'yan sunni suka fi karfafa hare-haren su ga sojojin tarbace da Amurka ke jagoranta. Sojin Amurka sun ce, harin zai kawai kara karfafa anniyar Amurka ne wajen tabbatar manufar ta a Iraqi. Sun ce rundunar Amurkan zata ci gaba da kasancewa a Iraqi har sai an 'yantar da kasar ta hanyar samar da tsaro da kwanciyar hankali.

XS
SM
MD
LG