Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firaministan    Iraqi  ya ce kokarin kafa  dimukuradiya - 2004-09-23


Firaministan rikon kwarya na Iraqi Iyad Allawi ya ce kokarin samar da zaman lafiya da tabbatar da dimukuradiya a Iraqi na samun nasara. Mista Allawi ya bayar da wannan bayaninne ranar Alhamis a jawabinsa ga taron hadin gwiwa na majalisar dokokin Amurka a Washington.

Shugaban Iraqin ya kuma sha alwashin samun nasara kan ‘yan tawaye wadanda ke da alhakin kashe daruruwan mutane a Iraqi.Ya ce za a yi zaben da aka shirya yi a cikin watan Janairu kamar yadda aka shirya wanda zai bude hanyar samar da gwamnati wadda za ta samu karbuwa a wurin mutanen duniya dana Iraqi .

Mista Allawi ya godewa Amurka saboda hambarar da Sadddam Hussein daga kan mulki ya ce sadaukar da kan Amurka a Iraqi ba za zai zama a banza ba. Mista Allawi na fadar gwamnatin Amurka White House domin tataunawa da shugaba Bush.

XS
SM
MD
LG