Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush ya kare matakin Amurka na mamaye Iraqi... - 2004-09-23


Shugaba Bush ya kare matakin Amurka na mamaye Iraqi a jawabinsa ga babban taron majalisar dinkin duniya ranar talata a inda ya nemi kasashen duniya da su yaki ta’addanci su kuma tabbatar da mulkin dimukuradiya.

Mista Bush bai ba da martani kai tsaye ba ga babban sakataren majalisar dinkin duniya , Kofi Annan wanda a makon da ya wuce ya ce mamaye Iraqi baya bisa ka’ida. Amma ya ce kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya yi kashedin mataki mai tsauri ga tsohuwar gwamnatin Iraqi idan ta ki bin kudurorin da aka yi a baya sannan ya ce kasashen kawance karkashin jagorancin Amurka ‘’sun aiwatar da bukatun duniya ne da suka dace kawai.’’

A jawabinsa kan abubuwa da dama, shugaban ya yi kira da kasashen duniya da su marawa gwamnatin da Amurka ke goyon baya a Iraqi da Afganistan a lokacin da ‘yan ta’adda su ke kokarin kawo cikas a zabubbuka masu zuwa.

‘Muna tsammanin samun hare-haren ta’addanci a lokacin da Afganistan da Iraqi suke jiran zabubbukan kasa.Saboda haka aikin da ke gaba babba ne. ‘’Amma wadannan wahalhalu ba za su canja imaninmu ba cewa Afganistan da Iraqi suna da kyakkyawan fata na ‘yanci a gaba. Hanyar da ta fi dacewa a tinkari wahala ita ce ta ci gaba da abinda ake yi ba dakatawa ba.’’

Shugaban ya yi alkawarin tabbatar da ganin cewa mutanen Afganistan da Iraqi sun cika burinsu na samun ‘yanci da tsaro ya kuma ce wadannan kasashe za su zama abin kwaikwayo a gabas ta tsakiya inda ya ce ake hana miliyoyin mutane ,yanci da kuma hana su samun adalci.

Shugaban ya ce kasashe da dama har da Amurka suna hakuri kuma suna kau da kai daga danniyar da ake a gabas ta tsakiya da sunan samar da zaman lafiya. Ya ce sauye-sauye na dimukuradiya su ne hanyar da suka dace wajen kawo karshen rikicin Isra’ila da Falasdinawa sannan ya ce bangarorin biyu na da rawa wajen samun cimma burin shirin duniya na taswirar zaman lafiya. ‘’Kasashen larabawa su kawo karshen angiza mutanensu a kafofin watsa labaransu su kuma tsayar da bada kudi ta kowace hanya domin aikin ta’addanci sannan su dawo da huldar jakadanci da Isra’ila’’, in ji shugaban.

Isra’ila ta dakatar da maganar gina matsugunai sannan ta rushe wuraren duba mutane wanda basa bisa ka’ida kuma ta kawo karshen cin mutuncin Falasdinawa da kuma guji duk wani abu da zai iya kawo matsala ga tattaunawa ta karshe.

Mista Bush a kokarin nuna manufar gwamnatinsa kan al’amuran duniya ya ce manufar ta wuce harkar gabas ta tsakiya ya kuma yi wa kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya murna kan kudurinsa na makon jiya kan rikicin Darfur a Sudan ya kuma yi kira ga Sudan da ta girmama yarjejeniyar dakatar da bude wuta wanda ta rattaba hannu a kai a watan Afrilu ta kuma ‘tsayar da kashe –kashe a Darfur.’

Ya kuma jaddada kudurin Amurka kan yaki da yaduwar kwayoyin cutar kanjamau da fataucin mutane da cin hanci da kuma goyon baya ga bayar da taimako ga kasashe masu tasowa maimakon bayar da bashi da kuma goyon baya ga matakin kasar Costa Rica na haramta dashen dan tayi na bil Adama. Mista Bush ya ce bunkasar ‘yanci ita ce hanyar da za a samu zaman lafiya da ci gaba a duniya ya kuma kawo shawarar kafa asusun kula da dimukuradiya a karkashin majalisar dinkin duniya domin mutunta dokoki da kuma inganta cibiyoyin kula da dimukuradiya.

XS
SM
MD
LG