Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rumsfeld na tababa kan sace makaman Iraqi - 2004-11-01


Sakataren tsaron Amurka Donald Rumsfeld ya nemi cewa kada a yi gaggawar yanke hukunci kan bacewar ton dari hudu na nakiyoyi a Iraqi.

A cikin ‘yan kwanakinnan wannan matsala ta bacewar wadannan nakiyoyi ta zama babban batu a yakin neman zaben shugaban kasa a Amurka a inda dan takarar Democrat, John Kerry yake zargin gwamnatin Bush da sakaci wurin tabbatar da tsaronsu. Shi kuwa shugaba Bush ya mayar da martani cewa har yanzu ba a gama gano abinda ya faru ba.

Jami’an ma’aikatar tsaron Amurka sun fitar da wani hoto na sirri dake nuna wasu motoci a wurin da nakiyoyin suka bace. To ammma har yanzu basu nuna takamemen lokacin da aka kwashe su ba ko kuma shaidar cewa sojojin Iraqi ne suka kwashe su ba ko kuma cewa sace su aka yi bayan faduwar gwamnatin Saddam a bara.

Gwamnatin rikon kwarya ta Iraqi ta sanar da hukumar kula da yaduwar makaman kare dangi ta duniya ne batan wadannan makaman a farkon wannan watan .A kokarin janye siyasa daga maganar, sakataren tsaro Rumsfeld ya yi kokarin jawo hankalin dan takara John Kerry cewa yawancin rahotanni na farko kan al ‘amura sukan kasance ba dai-dai ba. ‘Batun cewa ba a dade da sace wadannan nakiyoyi ba abu ne da ke bukatar tattaunawa kamar yadda Amurka za ta yi domin Saddam ya kwashe wasu makamai a lokacin da ya ga yaki ya gabato’’, ya ce.

A ranar litinin jaridar The New York Times da kuma gidan talabijin na CBS suka ruwaito cewa wadannan nakiyoyi sun bace ne daga wani sansanin soja a kudancin Bagadaza kuma ya kamata su zama suna karkashin kulawar sojojin Amurka tun bayan mamayewar da Amurka ta yi wa Iraqi.

XS
SM
MD
LG