Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bush da Kerry Sunyi ta Yakin Neman Zabe ba Dare ba Rana - 2004-11-02


An bude runfunan zabe a duk fadin Amurka, yayinda milyoyin jama'a ke kada kuri'a a zaben shugaban kasar da akafi fafatawa a gareshi. Kuri'ar jin ra'ayin jama'a da aka gudanar a jajibirin zaben ya nuna al-ummar kasar sun rabu daidai-wa-daida a tsakanin yan takarar jam'iyar Republican, Shugaba Bush da abokin fafatawar sa na damokarat, John kerry.

Jama'a sun nuna shawa sosai a zaben da masana suka yi hasashen cewa za'a samu fitowar mutanen da ba'a taba gani ba ko kuma ma masu zabe sama da milyan 120 zasu kada kuri'a a duk fadin kasar. Dukkan 'yan takarar biyu, shugaba George Bush da John Kerry sunyi gangamin yakin neman zabe da dama a kwanakkin karshen da suka rage kamin zaben a jihohin da dama na kasar. sun mayar da hankali ne a jihohin da suka fi mahimmanci, wadanda ake ganin ba wata tazara a tsakanin su.

Da safiyar yau talata ne, shugaba Bush da uwargidan sa da 'yayan sa mata biyu suka kada kuri'ar su a runfar da suka saba yin zabe a garin su dake Texas. Bayan jefa kuri'ar sa, shugaba Bush ya zanta da 'yan jarida. Ya sheda musu cewa " Na yarda da matakin ko hukumcin da mutanen Amurka zasu dauka. Ina matukar begen damokaradiyar mu. Na yi imani da hangen nisar mutanen kasar nan."

Shugaban kasar ya yada zagon na karshe a jihar Ohio kamin ya zarce zuwa fadar white house inda zai saurari bayanen sakamakon zaben. A wani abun da ya kauce ma al'ada, 'yan takarar biyu sun ci gaba da yakin neman zabe a ranar zaben, wanda hakan ya nuna irin yadda zaben yake kud-da-kud.

Sanata Kerry ya kashe daren jiya a jihar wisconsin mai mahimmanci a sakamakon zaben inda ya dinga baiwa masu aikin sa kai na zaben kayan aikin zaben. Bayan haka kuma da safiyar yau talata, shi da kan sa ya dinga raba takardun bayanen manufofin sa ga masu aikin yakin neman zaben sa. 'Yan takarar su biyu sun gudanar da gagarumin yekuwar ganin magoya bayansu sun fito sun yi zabe. Yace "yanzu ne lokacin da damokaradiya mafi karfi da tasiri a doron duniya zata nuna ma al-ummar duniya yadda muke aiki. Kuma tare mu 'yan kasar zamu sauya alkiblar wannan kasar." Wakilin Muryar Amurka wanda yake cikin ayarin kampe din John Kery, ya ce ya lura Sanata Kerry ya natsu yau talata. Da takarar na Jam'iyar Damokarat ya ma yi ta ba'a da wasa da 'yanjarida, har ma ya dauki hoto dasu kamin ya dana jirgin sa ya wuce zuwa Boston inda zai kada kuri'ar sa da rana.

'Yan takarar biyu sun bayana kwarin gwiwar zasu lashe zaben. Sai dai mataimakin dantakarar shugaban kasa John Kerry, Mr John Edwards ya ki ya yi wani takamaiman hasashen zasu ci zaben a lokacin da ya bayana a wani shirin gidan talabijin na NBC, abun da ke nuna yadda zaben yake gab-da-gab.

XS
SM
MD
LG