Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An sake zabar shugaba Bush - 2004-11-03


Shugaba Bush ya sake lashe zaben shugabancin Amurka a karo na biyu. Bayan wani tsawon lokaci da kammala zaben a daren ranar talata senata Kerry ya kira shugaba Bush a safiyar laraba a inda ya amince da shan kaye a zaben. Tattaunawar da suka yi gajeriya ce, kasa da minti biyar kuma mataimakan Kerry na yakin neman zabe da kuma ma’aikatan White House sun bayyana tattaunawar cike da karamci. Wannan ya biyo bayan wani lokaci ana kidayar kuri’u a mahimmiyar jihar Ohio.. Shugaba Bush ya yi nasara a yawan gundarin kuri’u da kuma yawan wakilan masu tantance wanda ya ci zabe , wanda shi ya tabbatar da wannan nasarar.

John Kerry Ana sa ran senata Kerry zai yi jawabin tabbatar da rungumar kayen zaben nan ba da dadewa ba a inda jawabin samun nasara za ta biyo baya daga bakin shugaba Bush.

Dukkanin alamu sun nuna cewa shugaban zai yi amfani da jawabin ya godewa dan takarar Democrat saboda kykkyawar takara. Dan takarar Republican din wanda ya samu nasarar a karo na biyu za ‘a rantsar da shi a watan Janairu kuma ana san ran zai yi kokarin dinke duk wata baraka da ta bullo kai a lokacin kamfen.

Zaben ranar talatar ya zama babbar nasara ga ‘yan Republican a duk inda suke domin bayan samun damar ci gaba da rike fadar gwamnati ta White House jam’iyyar shugaban ta kara karfi a dukkanin majalisun kasar guda biyu.

XS
SM
MD
LG