Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Arafat ya rasu yana da shekaru saba’in da biyar - 2004-11-11


Yasser Arafat ya rasu. An sanar da rasuwarsa da safiyar Alhamis a Faransa inda ya kwanta jinya na wasu kwanaki. Jami’an Palasdinawa da kuma na asibitin Percy da ke wajen Paris ne suka bayyana mutuwar tasa. Sanarwar asibitin ta ce shugaban Palasdinawan dan shekaru saba’in da biyar ya rasu ne da safiyar Alhamis. Bayan ya sha doguwar jiyya na mutu-kokai-rai- kokai yanayin jikinsa ya tsananta inda aka ce kwakwalwarsa ta daina aiki ko kuma ma ya mutu kafin ya rasu a yau Alhamis.

Abinda ya jawo misayar yawu tsakanin uwargidansa Shua da kuma sauran shugabannin Palasdinawa. Za a dauki gawarsa zuwa Alkahira don a yi mata jana’iza daga nan kuma a kai ta Ramallah da ke yammacin bakin kogi don binnewa bayan da jami’an Isra’ila suka amince da wannan shirye-shiryen.

Arafat ya kasance wanda ake gani ta fuskoki daban-daban---wasu suna ganinsa jarumi kuma shugaba wasu kuma suna daukarsa dan ta'adda. Mutuwarsa za ta jawo hankali kan wa zai gaje shi da kuma makomar shirin samar da zaman lafiya a gabas ta tsakiya.

XS
SM
MD
LG