Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush  ya ce dole Iran ta dakatar da shirin kera makaman kare dangi - 2004-12-01


Shugaba Bush na Amurka ya ce matakin kasar Farisa na jingine shirinta na inganta ma ’adinin Uranium abu ne mai kyau sai dai ba shine karshen maganar ba . A taron hadin gwiwa da ‘yan jaridu a Kanada ranar talata , Mista Bush ya ce dole ne Farisa ta kara sa himma wajen lalata shirinta na kera makaman kare-dangi. Ya kuma ce dole duniya ta sa ido don tabbatar da cewa Farisa ta cika alkawarinta.

A ranar litinin Farisa ta amince da ta dakatar da shirinta na kera makaman kare-dangi bayan cimma yarjejeniya da masu sa baki na kasashen turai. Wannan yarjejeniya ta sanya dakatar da yunkurin Amurka na kai batun gaban kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya don aza mata takunkumi. To amma ita Farisa ta ce ba ta bar ‘yancinta na ingnata ma’a dinin Uranium gaba daya ba ne ta kuma ce yarjejeniyar za ta kare cikin watanni

XS
SM
MD
LG