Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An samu rashin fitowar jama'a a zaben yankin Warri - 2004-12-03


A shiga rana ta biyu a zaben da ake yi a garin Warri mai arzikin man fetur kuma wanda ake fama da rikice-rikice a cikinsa cikin tsattsauran matakan tsaro. Sai dai a rana ta biyun babu fitowar mutane da yawa a zaben kananan hukumomi uku na cikin birnin. An daga zaben saboda rashin kayayyakin zabe a yawancin wuraren jefa kuria'a a ranar Alhamis.

Wasu masu son jefa kuri'a da dama sun ce ba su gano inda za su jefa kuri'unsu ba.Duk da irin wannan matsaloli, masu aikin zabe sun ce suna fata duk masu son jefa kuri'a za su samu damar yi. Mafi yawancin 'yan takara a karkashin jam'iyyar PDP suna takararne ba da hamayya ba abinda ya sanya zaben ba ya yiwuwa a wurare da dama.Shugabannin 'yan kabilar Ijaw sun nemi da a kauracewa zaben gaba daya don suna zargin cewa jam'iyya mai mulki da kuma 'yan kabilar Itsekiri sun zana yankunan zabe don ya basu wata dama a kansu. Alex Vines, wani mai sharhi daga London wanda ya zo Najeriya kwanan baya ya ce tarin jami'an tsaro da kuma matasan kungiyoyi ya hana wasu masu son jefa kuri'a fitowa su jefa kuri'unsu.

'Akwai tursasawa da cin zali akwai kuma kananan makamai a hannun matasa, wannan zai hana samun cikakkiyar dimukuradiyya. An yi zaben kananan hukumomi a duk fadin Najeriya a watan Maris amma aka daga na Warri saboda tsoron tashin hankali. Dubannin mutane ke mutuwa a duk shekara sakamakon rikice-rikice na kabilanci da sauran laifuffuka a wannan yanki mai arzikin mai da ke yankin Neja -Delta na kudancin Najeriya.

XS
SM
MD
LG